Isa ga babban shafi
Amurka-Saudi

Trump ya nesanta kansa da kokarin kare Saudia a bacewar Khashoggi

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta zargin da ake masa na goyon bayan Saudi Arabia game bacewar dan Jarida Jamal Khashoggi, inda ya yi ikirarin bayyana gaskiyar halin da ake ciki nan da kwanaki kadan.

Sai dai Jaridar Washington Post da ke Amurka ta zargi Donald Trump da yunkurin badda sawu dangane da zargin kisan dan jaridar domin kare gwamnatin Saudiyyar.
Sai dai Jaridar Washington Post da ke Amurka ta zargi Donald Trump da yunkurin badda sawu dangane da zargin kisan dan jaridar domin kare gwamnatin Saudiyyar. 路透社图片
Talla

A zantawarsa da manema labarai a fadar White House Trump ya ce ko kadan baya goyon bayan Saudiyya don samar mata da mafaka a zargin kisan dan Jaridar wanda ya bace kawo yanzu ba a kai ga gano shi ba.

A cewar shugaban zai samu cikakken bayani daga bakin sakatarensa Mike Pompeo wanda yanzu haka ke ganawa da shugabannin Saudi dana Turkiyya game da bacewar dan jaridar dama zargin kisanshi da ake kan kasar ta Saudi Arabia.

Sai dai Jaridar Washington Post da ke Amurka ta zargi Donald Trump da yunkurin badda sawu dangane da zargin kisan dan jaridar domin kare gwamnatin Saudiyyar.

A sharhin da ta wallafa, Jaridar ta yi tambaya kan dalilin da shugaba Trump ke kokarin kare aika aikan da gwamnatin Saudiya ta yi, inda ta bayyana goyan bayan ta ga matsayin Majalisar Dinkin Duniya na kafa kwamitin kasashen duniya da zai gudanar da bincike kan lamarin.

Jaridar ta ce kalaman Trump na cigaba da bayyana aniyar sa na kare Saudiya daga laifin da ta yi wajen bacewar Khashoggi wanda ya ke mata rubutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.