Isa ga babban shafi
Maroko-Tarayyar Turai

Maroko ta gargadi Turai kan gina katangar tare bakin-haure

Ministan harakokin wajen kasar Maroko Nasser Bourita ya gargadi kasashen turai kan niyar da suke da ita na shata Katanga domin hana bakin haure shiga nahiyar, wanda hakan zai kara haifar da matsaloli ga kasashen da matafiya ke ratsawa ta cikinsu zuwa nahiyar ta turai

ministan harakokin wajen Maroko Nasser Bourita na yiwa taron majalisar dinkin duniya karo na  72 jawabi.  New York, U.S., 20 September  2017.
ministan harakokin wajen Maroko Nasser Bourita na yiwa taron majalisar dinkin duniya karo na 72 jawabi. New York, U.S., 20 September 2017. REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran AFP ministan harakokin wajen na Maroko M. Bourita ya ce matsawar turai ta zabi tsare kanta ita kadai zai taimaka wajen kara samun kwarar bakin haure, matsawar kuma turai ta zabi killace kanta da Katanga a kwai sabin dubaru da za bullo dasu wajen kaucewa saka idon jami’an tsaronta

Don haka bai dace ba, a kara dora nauyi kan kasashen da bakin hauren ke ratsawa ta cikinsu tare da kara azabtar da su. Inda ya kara da cewa, matsalar kwararar bakin haure matsala ce da ta shafi kowa, kuma ya kamata daga kasashen na turai da ma wadanda ake ratsawa ta cikinsu ya dau nauyin da ya rataya a wuyansa.

Kasar Maroko dai, kasa ce da yan kasashen Afrika ke shiga ba tare da visa ba, ta kuma zama wata babbar turba ga bakin hauren dake yiwa nahiyar turai shigar burtu ta teku.

A cewar kungiyar dake kula da tafiye tafiye ta MDD OIM kimanin matafiya dubu 42.500 ne tun farkon wannan shekara ta 2018 kawo yau suka kutsa kai kasar Spain ta teku, adadin da ya rubanya sau 3 idan aka auna da wadanda suka suka shiga kasar a 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.