Isa ga babban shafi
London

An garkame Assange a gidan yarin London

An garkame mamallakin shafin WikiLeaks da ke kwarmata bayanan sirri, Julian Assange a gidan yarin Birtaniya, yayinda ake ganin akwai yiwuwar a tasa keyarsa zuwa Amurka domin fuskantar hukunci saboda fallasa bayanan sirrinta.

Julian Assange lokacin da ya shiga hannun 'yan sandan Birtaniya
Julian Assange lokacin da ya shiga hannun 'yan sandan Birtaniya REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Wannan na zuwa ne bayan jami’an ‘yan sanda sun cafke Assange da ke samun mafaka a ofishin jakadancin Ecuador da ke birnin London, in da ya kwashe shekaru bakwai yana buya.

Assange mai shekaru 47 kuma dan asalin kasar Australia, ya bayyana a gaban kotu bisa zargin sa da laifin karya sharuddan belinsa a shekarar 2012 a Birtaniya, yayinda yake fuskatar yiwuwar tasa keyarsa zuwa Amurka nan gaba.

Bayan jami’an ‘yan sandan Birtaniya sun kama shi a jiya Alhamis, hukumomin Amurka suka bayyana shirinsu na tuhumrsa kan zargin sa da fallasa bayanan sirrin kasar bayan wani kusten kamfuta.

A halin yanzu ana ci gaba da tsare Assange a gidan yarin Wandsworth da ke kudancin birnin London, in da a can baya ya taba kwashe kwanaki 9 a cikinsa bayan tuhumar sa kan laifin cin zarafin wata mata a Sweden, batun da tuntuni aka ajiye shi.

Kazalika akwai yiwuwar Assange ya fusknci hukuncin daurin shekara guda a gidan yarin na London, yayinda a gefe guda, kotun Westminister za ta sake wani zama a ranar 2 ga watan Mayu mai zuwa domin yanke hukunci kan batun tasa keyarsa.

Kodayake lauyar da ke kare shi, Jennifer Robinson ta ce, za su kalubalanci batun tasa keyarsa zuwa Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.