Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun hadin-guiwa sun kashe mutane kusan dubu 2 a Raqa

Wani rahoto ya ce luguden wuta kan birnin Raqa da dakarun hadin-guiwa, karkashin jagorancin Amurka suka yi a shekarar 2017, ya kashe fararen hula dubu 1 da dari 6 cikin watanni 4.

Wani hari da Amurka ta jagoranta wajen kaddamarwa a Raqa
Wani hari da Amurka ta jagoranta wajen kaddamarwa a Raqa ©BULENT KILIC / AFP
Talla

An tattara sakamakon ne bayan shafe watanni ana bincike tare da tattara bayanai, har ma da wani shiri na musamman na karbar bayanan da ‘yan gwagwarmaya ta kafofin sadarwar zamani su dubu 3 suka tattaro kamar su hotuna ta tauraron dan adam.

A tsakiyar shekarar 2017, birnin Raqa ya kasance tamkar shalkwatar daular kungiyar IS, kuma shekaru uku dakarun hadin-guiwan da Amurka ke jagoranta suka yi suna luguden wuta a kan birnin don kakkabe ‘yan ta’adan.

Rahoton na kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty tare da hadin guiwan Aiwars Monitor Group, ya bukaci dakarun kawancen da su gudanar da ayyukansu bisa doka da oda.

A cewar rahoton, akasarin luguden wutar da aka yi ba su fada inda aka yi niyya ba, kuma dubun-dubatan hare-haren da aka kai da manyan bindigogin artillery an yi su ne kan mai uwa da wabi.

Dakarun hadin-guiwan sun amince da laifin salwantar rayuka na kashi 10 ne kawai a mace-macen da luguden wutar ya haddasa, amma Kungiyar Amnesty da kungiyar sa ido na Airwars ta yi kira gare su da kawo karshen musanta kasancewa da hannu dumu-dumu a barnata dukiya da dimbim rayuka a Raqa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.