Amurka ta janye takunkumin da ta kakaba wa Turkiya
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da dage takunkumin karayar tattalin arziki da ya kakaba wa Turkiya, inda kuma ya kare kansa daga daukar matakin janye dakarunsa daga Syria.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya bukaci Hukumar Baitul-malin Amurka da ta cire dukkan takunkumin da aka malkaya wa Turkiya a ranar 14 ga wannan wata na Oktoba saboda hare-haren da gwamnatin RecepTayyip Erdogan ke kaddamarwa kan mayakan Kurdawa a yankin arewa maso gabashin Syria.
A cewar Trump "wannan takunkumin zamu cire shi, sai idan har an sake samun wata matsalar da ba mu ji dadi ba".
"Na yi magana da jagoran Kurdawa, kuma ya nuna matukar godiya saboda matakin Turkiya na dakatar da hare-harenta". In ji Trump.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu