Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Dumamar yanayi na haddasa rikici tsakanin al'umma

Wani binciken masana ya bayyana sauyin yanayi a matsayin babbar matsalar da ke haifar da tashe-tashen hankula da kuma rashin hadin ka tsakanin al’ummomi, bayan kwashe dogon lokaci ana fama da rikici a Somalia.

Wani yanki da sauyin yanayi ya haifar wa fari
Wani yanki da sauyin yanayi ya haifar wa fari រូបភាព​ឯកសារ
Talla

Binciken da Cibiyar Wanzar da Zaman Lafiya ta Stockholm ta gudanar, ya yi nazari  kan rawar da ofishin Majalisar Dinkin Duniya ke takawa a Somalia da kuma illar da sauyin yanayi ke yi, in da ya yanke hukuncin cewar matsalar na matukar tasiri wajen haifar da rigingimu.

Florian Krampe, babbar mai bincike a cibiyar ta ce, matsalar fari ta zafafa rikicin Somalia ganin yadda aka kwashe dogon lokaci ana fama da karancin ruwan sama.

Binciken ya ce, fari da ambaliya sun tilasta wa dubban mutane barin matsugunansu zuwa sansanonin da ake dibar su wajen shiga ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.