Isa ga babban shafi

Sabuwar zanga-zangar Iraqi ta hallaka gomman mutane

A kasar Iraqi masu zanga-zangar adawa da Gwamnati sun cinnawa babban Ofishin gunduman Dhi Qar wuta , yayinda rayukan mutane fiye da goma aka tabbatar da mutuwarsu a yau, yayin da wasu akalla 100 suka jikkata a lokacin da ‘yan sanda suka harba barkonun tsohuwa yayin tarzoman a birnin Bagadaza.

Jami'an tsaron Iraqi gaban masu zanga-zanga a kasar
Jami'an tsaron Iraqi gaban masu zanga-zanga a kasar REUTERS/Thaier Al-Sudani
Talla

Dubban Masu boren dai sun yi ta bayyana fushinsu da tsaban cin hanci da matsanancin halin rayuwa da rashin ayyukan da suka addabi jama'a.

Samada mutane 150 ne dai suka rasa rayukansu a boren gamagarin da ake yi a fadin kasar tun a farkon wannan wata.

A hudubar da ya gabatar a yau, jagoran mabiya Shi'a na kasar Ayatollah Ali al-Sistani ya roki masu boren da su wa Allah su bi a sannu, gudun kada lamarin ya kazance sosai, yayin da ya bukaci jamian tsaro da suma subi da lalama.

Hudubar tasa dai ta tsaya ne kan jerin sauye-sauyen da Franminista Adel - Abdel Mahdi ya gabatar ne na yaki da cin hanci da rashawa, samar da ayyukan yi da kuma samar da muhimman kayayyakin more rayuwa.

A ranar Juma'a dai Abdel ke cika shekara daya, da kwana daya bisa madafun iko, wanda yazo daidai da cikan wa'adin da jagoran shi'a na kasar ya bayar don Firanministan ya yi sauye-sauyen da suka dace don jama'a su ci moriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.