Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Turkiya da Faransa sun nemi a tsagaita wuta a yankin Indlib na Syria

Kasashen Turkiya da Faransa sun bukaci tsagaita wuta a luguden da hadakar Sojin Syria da na Rasha ke yi a marika ta karshe da ke hannun ‘yan tawayen Syria a yankin Idlib.

Luguden wutar da Sojin Rasha da Syria ke yi a yankin Idlib.
Luguden wutar da Sojin Rasha da Syria ke yi a yankin Idlib. Abdulaziz KETAZ / AFP
Talla

Cikin makwanni baya-bayan nan akalla farafen hula 80 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da 8 a yammacin jiya Talata da suka kunshi kananan yara 5, duk dai sakamakon luguden wutar da Sojin na Syria da hadin gwiwar Rasha ke ci gaba da yi yankin na Idlib wanda ta tilastawa fiye da mutum dubu 40 tserewa daga muhallansu.

Yanzu haka dai Turkiya karkashin jagoranci Recep Tayyib Erdogan ta aike da tawaga ta musamman Rasha don kawo karshen hare-haren inda kakakin gwamnatin kasar Ibrahim Kalin ke cewa ana bukatar sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta maye gurbin ta watan Agusta.

Wannan ne dai karon farko cikin shekarar nan da aka samu yawaitar fararen hula da ke tsallaka iyakar ta Syria galibi Turkiya don tsira da rayukansu.

A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Birtaniya mai sanya idanu kan rikicin na Syria, hare-haren Sojin na Syria da Rash aya shafi tarin makarantu da asibitoci yayinda ya tashi kauyukan Jubas da Saraqeb da ke kudancin Idlib.

Itama dai ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce akwai bukatar tsagaita wuta a hare-haren don bayar da kariya ga rayukan fararen hula da ke ci gaba da salwanta a kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.