Isa ga babban shafi
Iraq

Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofishin Amurka

Dubban masu zanga-zanga sun kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Baghdad na Iraqi, inda suka keta katangar harabar ofishin tare da rera wake-waken da ke cewa ‘ Mutuwa ta tabbata ga Amurka’. Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta kaddamar da hare-haren jiragen sama kan sansanonin mayakan Hezbollah a Iraqi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na kona tutar Amurka a harabar ofishin jakadancin kasar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar na kona tutar Amurka a harabar ofishin jakadancin kasar. REUTERS/Alaa al-Marjani
Talla

A karon farko kenan cikin tsawon shekaru da masu zanga-zangar suka samu damar isa ofishin jakadancin Amurka da ke wani yanki mai cike da tsaro, inda suka tsallake shingayen binciken ababawan hawa.

Wani dandazon maza sanye da kakin soja da kuma ayarin mata sun yi tattaki har zuwa katanagar ofishin jakadancin ba tare da wani jami’in tsaro ya dakatar da su ba.

Masu zanga-zangar sun yi ta cilla duwatsu, yayin da suka banbare kyamarorin da aka makala a jikin ginin ofishin jakadancin na Amurka.

Kodayake jami’an sojin ruwan Amurka da ke cikin ofishin sun harba wa masu zanga-zangar hayakai mai sa kwalla domin tarwatsa su, yayin da shugaba Donald Trump ke cewa, ya yi zaton gwamnatin Iraqi za ta yi amfani da dakarunta wajen kare ofishin jakadancin.

Shugaba Trump ya kuma zargi kasar Iran da kitsa kai hari kan ofishin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jiragen yakin Amurka suka yi luguden wutar da ya kashe mayakan Hezbollah 25, farmakin da ake kallo a matsayin ramuyar gayya kan jerin hare-haren rokokin da suka yi sanadiyar mutuwar wani Ba’amurke guda a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.