Isa ga babban shafi
Kenya

Al-Shebaab ta kashe Amurkawa uku a Kenya

Mayakan Al-Shebaab na Somalia sun kaddamar da farmaki kan sansanin sojin da Amurka ke amfani da shi a Kenya, inda suka kashe Amurkawa uku tare da lalata jirgin sama da motocin yaki kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar.

Sojin Kenya a kusa da sansanin Lamu da al-Shebaab ta kai hari kan Amurkawa
Sojin Kenya a kusa da sansanin Lamu da al-Shebaab ta kai hari kan Amurkawa REUTERS/Stringer
Talla

An kashe sojin Amurka guda da kuma wasu Amukawa biyu ‘yan kwangila.

Bayanai na cewa, akalalla akwai sojojin Amurka 150 da ke zama a sansanin, inda suke bayar da horo ga dakarun gabashin Afrika da ke yaki da ta’addanci.

A ranar Lahadi ne maharan suka keta wannan sansani mai cike da tsaro da ke yankin Lamu na Kenya, amma an kashe hudu daga cikinsu kamar yadda mai magana da yawun sojin kasar, Kanar Paul Njuguna ya bayyana.

Yankin Lamu wanda ke kusa da kan iyakar Somalia, na dauke da wani shaharren tssibirin shakatawa, kuma ya sha gamuwa da jerin hare-haren ta’addanci.

Tun lokacin da Kenya ta aika dakarunta zuwa kasar Somalia a shekarar 2011, mayakan Al-Shebaab suka fara kaddamar mata da hare-hare babu kakkautawa.

Kenyar ta tura dakarunta zuwa Somalia ne karkashin dakarun Afrika da ke kare gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kasashen duniya, gwamnatin da Al-Shebaab ke fafutukar hambararwa.

Babban Sufeta Janar na ‘yan sandan Kenya, Hilarry Mutyambi ya ce, jami’an tsaro na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wannan farmaki.

Jami’an sojin Amurka sun tabbatar da farmakin, inda suka ce, sojojinsu da hadin guiwar na Kenya sun fatattaki mayakan na Al-Shebaab.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon barazanar da Iran ta yi mata ta ramuwar gayya kan kisan Janar Qassem Soulaimani a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.