Isa ga babban shafi
Faransa-Iraqi

Faransa ba ta da shirin janye dakarunta a Iraqi- Parly

Gwamnatin Faransa ta ce bata da shirin janye dakarunta daga Iraqi duk da fargabar abin da ka iya biyo bayan kisan da Amurka ta yiwa babban kwamandan Sojin Iran na ketare a filin jirgin saman birnin Bagadaza.

Ministar tsaron Faransa Florence Parly yayin ziyarar da ta kaiwa dakarun kasar da ke yaki a Iraqi da Syria.
Ministar tsaron Faransa Florence Parly yayin ziyarar da ta kaiwa dakarun kasar da ke yaki a Iraqi da Syria. Daphné BENOIT / AFP
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron faransa ta fitar ta ce cikin dakarunta 200 da ke tallafawa Amurka yaki da IS a kasar ta Iraqi, akalla 160 sun himmatu ne wajen baiwa sojin kasar horon yaki da ta’addanci yayinda 40 kadai ne ke fagen daga.

Sanarwar ta ruwaito ministar tsaron Faransa Florence Parly na cewa babu wani shiri akasa na yunkurin janye dakarun kasar daga Iraqi, maimakon haka za su sake karfafa yakin da take da mayakan IS.

A cewar Parly babu batun sauya matsaya har sai sun kammala fatattakar mayakan IS daga yankin gabas ta tsakiya.

Hadakar kasashen da ke tallafawa Amurka yaki da kungiyar IS a Iraqi dai na cike da tantama bayan harin na ranar Juma’a wanda ake da yakinin Iran za ta mayar da martani kowanne lokaci daga yanzu, yayinda itama Amurka kanta ke shirye-shiryen janye na ta dakarun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.