Isa ga babban shafi
Benin

Faransa ta mayar wa Benin kayayyakin tarihinta

Jakadun Faransa da na Japan sun cudanya da jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da kuma daliban makarantu, a daidai lokacin da Jamhuriyar Benin ta yi bikin murnar dawo mata da kayayyakin tarihin da Turawan Mulkin Mallaka na Faransa suka wawushe sama da shekaru 100 da suka gabata.

Wasu daga cikin kayayyakin tarihin da Faransa ta dawo wa da Benin
Wasu daga cikin kayayyakin tarihin da Faransa ta dawo wa da Benin france24
Talla

A yayin bikin maido da kayayyakin tarihin, baki sun yi cincirindo suna kallon kayatattacen takobin da wata tsohuwar gwarzuwar yaki ta sassaka tun karni na 19 a Benin. Sauran kayayyakin da aka maido da su sun hada da sandar sarki mai zubin gatari.

An maido da kayayyakin ne bayan Faransa ta amince ta mayar da wasu daga cikinsu, yayin da wata kungiya mai zaman kanta a kusa da birnin Paris ta yi tsayin daka wajen ganin an bai wa Benin kayayyakinta.

An dai yi bikin baje-kolin nau’uka 28 na kayyakin ne a wani karamin gidan tarihi na Petit Musee de la Recade da ke wajen birnin Cotonou.

Tun a birnin Paris na Faransa aka fara baje wadannan kayayaki a gidan tarihin Quai Branly, wanda ke dauke da dubun dubatan kayayyakin tarihin Afrika.

An sace kayayayyakin Benin ne a karshen karni na 19, lokacin da kasar ke amsa sunan Masarautar Dahomey kafin ta kasance karkashin cikakken ikon Faransa daga shekarar 1894.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.