Isa ga babban shafi
China-Corona

Mutanen da annobar Corona ke halakawa a China na karuwa

Ma’aikatar lafiyar China, ta ce duk da saukin yaduwar annobar murar Corona da aka samu, adadin wadanda cutar ta halaka na ci gaba da karuwa, inda a yanzu haka suka haura dubu 1 da 800.

Jami'an lafiya yayin kula da wadanda annobar murar mashako ta Corona ta shafa a wani asibiti dake birnin Wuhan a lardin Hubei, inda cutar ta soma bulla.
Jami'an lafiya yayin kula da wadanda annobar murar mashako ta Corona ta shafa a wani asibiti dake birnin Wuhan a lardin Hubei, inda cutar ta soma bulla. Chinatopix via AP
Talla

Kididdigar da hukumar lafiyar ta China ta fitar a yau talata ta nuna cewa zuwa daren jiya Litinin annobar murar mashakon ta Coronavirus ta halaka mutane dubu 1 da 868, bayan mutuwar karin mutane 93 a lardin Hubei inda cutar ta soma bulla.

Ma’aikatar ta kuma ce karin mutane dubu 1 da 886 ne suka kamu da cutar murar mashakon a baya bayan nan, kuma mafi akasarinsu daga lardin na Hubei, abinda yasa yanzu haka adadin jimillar wadanda annobar ta shafa a sassan kasar ta China kaiwa dubu 72 da 436.

A wannan talatar ce kuma rahotannin kafafen yada labaran kasar ta China suka ce sama jami’an lafiyar kasar dubu 3000 ne ake kyautata zaton sun kamu da cutar murar ta Corona, kusan niniki 2 adadin jami’an lafiyar dubu 1 da 716 da gwamnati ta ce annobar ta shafa a ranar 14 ga watannan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.