Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta ki yi wa al'ummar duniya sassauci

A kalla mutane miliyan 1 da dubu 35 ne suka harbu da coronavirus wadda ta lakume rayuka fiye da dubu 53 a kasashen duniya 188 tun bayan bullarta a kasar China a karshen shekarar bara.

Annobar coronavirus ta karade lungu da sako na duniya
Annobar coronavirus ta karade lungu da sako na duniya indiatimes
Talla

Italiya ce kasar da ta fi samun asarar rayukan mutane a sanadiyar coronavirus, inda ta rasa mutane dubu 13 da 915, yayin da Spain ke matsayi na biyu da asarar mutane dubu 10 da 935, sai kuma Amurka wadda cutar ta kashe mata mutane dubu 6 da 58, yayin da a Faransa aka samu mutuwar mutane dubu 5 da 387.

Rabin wadanda suka kamu da wannan annuba sun fito ne daga nahiyar Turai, sai kuma kashi daya bisa hudu da suka fito daga kasar Amurka kadai.

A bangare guda, an bude wani sabon asibitin wucen-gadi a wani dakin taro da ke gabashin birnin London wanda aka sanya masa sunan fitacciyar malamar jinyar nan da ta kafa tarihi a karni na 19 wato Florence Nightingale.

A cikin kwanaki 9 kacal aka samar da wannan asibitin wanda a tashin farko aka zuba masa gadaje 500, amma ana iya rubanya gadajen ninki ba-ninki har zuwa dubu 4.

Annubar coronavirus dai za ta iya haddasa wa tattalin arzikin duniya asarar zunzurutun Dala tiriliyan 4.1 a daidai loakacin da ta yi mummunar barna a Amurka da Turai da sauran kasashen duniya masu karfin tattalin arzaiki, kamar yadda Bankin Bunkasa Nahiyar Asiya ya yi gargadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.