Isa ga babban shafi
Ramadan

Za mu ci gaba da kai hari cikin watan Ramadan-Taliban

Kungiyar Mayakan Taliban ta yi watsi da tayin gwamnatin Afghanistan na tsagaita musayar wuta a cikin watan Ramadan, tana mai cewa, yarjejeniyar da aka gabatar mata ba ta da armashi, yayin da ta ci gaba da zafafa hare-harenta kan jami’an gwamnatin kasar.

Mayakan Taliban sun yi watsi da tayin jingine kaddamar da hare-hare cikin watan Ramadan duk da alfarmar watan.
Mayakan Taliban sun yi watsi da tayin jingine kaddamar da hare-hare cikin watan Ramadan duk da alfarmar watan. Reuters
Talla

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya roki mayakan da su ajiye makamansu saboda alfarmar watan Ramadan, baya ga annobar coronavirus da gwamatin kasar ke fafutukar yaki da ita.

Wani sakon Twitter da mai magana da yawun Taliban, Suhail Shaheen ya fitar, ya caccaki tayin da gwamnatin ta yi wa mayakan,inda suka ce, jinkirin musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu, shi ne babban dalilinsu na zafafa hare-hare a Afghanistan.

A farkon wannan shekarar ne, gwamnatin Afghanistan da Taliban suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin musayar fursunoninsu, amma har yanzu ba a kammala aiwatar da musayar ba, ballantana su hau teburin tattaunawar sulhu a tsakaninsu.

Ko a cikin wannan makon, sai da mayakan na Taliban suka kaddamar da farmakin da ya kashe jami’an tsaron Afghanistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.