Isa ga babban shafi
Duniya

Rashin hadin kai ne ya baiwa coronavirus damar addabar duniya - Guterres

Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya zargi gwamnatocin kasashe da kin hada kai wajen yakar annobar coronavirus da kawo yanzu ta addabi duniya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner
Talla

Yayin tsokaci kan halin da duniyar ke ciki, Guterres yace rashin hadin kan ne ya baiwa annobar damar yaduwa cikin sauki, gami da kashe dubban rayuka, yanayin da yace tilas ya razana kowa.

00:39

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kan rashin hadin kasashe

Nura Ado Suleiman

Binciken kwarraru a fannin kimiyya ya cimma matsayar cewar cutar coronavirus ta samo asali daga dabbobi zuwa ga dan Adam, wadda ta bulla a watan disambar shekarar 2019 a wata kasuwar saida naman dabbobi dake birnin Wuhan a China.

A baya bayan nan hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci hukumomin China da su bata damar hada gwiwa da kasar don karin bincike na musamman kan asalin cutar ta coronavirus da addabi duniya, bayanda a kasa da watanni 5 ta halaka sama da mutane dubu 235 da 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.