Isa ga babban shafi
India-Bangladesh

Guguwar Amphan ta raba akalla mutane dubu 50 da muhallansu a India da Bangladesh

Hukumomin India da Bangladesh sun soma aikin gyara yankunan da kakkarfar guguwar Amphan ta dai-daita bayan afka musu tun a jiya Laraba.

Yadda sararin samaniyar birnin Kolkata dake India ya murtuke, bayanda guguwar Amphan ta afka masa.
Yadda sararin samaniyar birnin Kolkata dake India ya murtuke, bayanda guguwar Amphan ta afka masa. DIBYANGSHU SARKAR / AFP
Talla

Masana sun ce guguwar ta Amphan itace mafi karfi da ta afkawa yankunan na India da Bangladesh tun bayan wadda aka gani a shekarar 1999.

Yanzu haka mutane 88 aka tabbatar da mutuwarsu a dalilin guguwar, wadda ta bazar da dubban gidaje gami da tuge bishiyoyi da turakan lantarki.

Ofishin lura da ayyukan Jinkai na Majalisar dinkin duniya yace akalla mutane miliyan 10 guguwar ta shafa, daga cikinsu kuma kimanin dubu 50 sun rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.