Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sauya matsaya kan hana daliban ketare bizar karatu a Amurka

Gwamnatin Amurka ta sauya matsayin ta dangane da hana dalibai daga kasashen ketare bizar zuwa kasar domin ci gaba da karatu sakamakon annobar COVID-19.

Shugaba Donald Trump na Amurka.
Shugaba Donald Trump na Amurka. AFP
Talla

Wannan ya biyo bayan maka gwamnatin a kotu da Jami’ar Havard da MIT da kungiyar malamai da kuma wasu Jihohi 18 na kasar suka yi domin kalubalantar matakin da shugaba Donald Trump ya dauka ranar 6 ga watan nan na hana bakin zuwa kasar.

Mai shari’a Allison Burroughs ya shaidawa mahalarta kotun cewar gwamnatin Amurka ta amince ta janye dokar saboda haka babu dalilin cigaba da shari’ar.

Akalla dalibai baki sama da miliyan guda yanzu haka ke karatu a Amurka, inda a kowacce shekara ake samu kaso mai yawa ke shiga kasar kowacce shekara don neman guraban karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.