Isa ga babban shafi
Amurka-ICC

Amurka ta kakabawa babbar jami'ar kotun duniya takunkumi

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da kakabawa babbar mai gabatar da karar kotun duniya ta ICC Fatou Bensouda takunkumai, ciki har da haramta mata shiga kasar.

Babbar jami'ar kotun duniya ICC mai gabatar da kara, Fatou Bensouda daga bangaren hagu
Babbar jami'ar kotun duniya ICC mai gabatar da kara, Fatou Bensouda daga bangaren hagu POOL/AFP/File
Talla

Matakin Amurkan dai martani ne kan binciken da kotun duniyar ta kaddamar kan zarge-zargen da ake yiwa dakarunta na aikata laifukan yaki a Afghanistan.

Yayin sanar da matakin na haramtawa Fatou Bensouda babbar jami’ar ta kotun ICC shiga Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, yace tuni sauka dauki irin wannan mataki kan wasu manyan jami’an kotun duniyar na haramta musu biza, kan binciken sojinsu dake Afghanistan bisa zarginsu da aikata laifukan yaki.

Pompeo wanda ya bayyana Kotun ICC a matsayin karen farautar wasu tsirarun kasashe, yayi gargadin idan har kotun za ta binciki sojojin Amurka a Afghanistan, to dukkanin kawayen dake taya ta yaki a kasar ma basu tsira daga abinda ta kira bita da kullin kotun duniyar ba.

Kakabawa babbar mai gabatar da karar ICC Fatou Bensouda da Amurka ta yin a zuwa ne yayinda ya rage watanni 2 a yi zaben shugaban kasar, wanda shugaba mai ci Donald Trump ke takarar neman wa’adai na 2, bayan kaurin sunan da yayi wajen kalubalantar hukumomin kasa da kasar da suka ki yin biyayya da bukatun Amurka.

Kamar dai wasu manyan kasashe ciki har da Rasha, China, Isra’ila, da Syria, Amurka ma ba mamba bace a karkashin kotun duniya, zalika ta dade tana adawa kotun ta ICC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.