Isa ga babban shafi
Iran-Iraqi

Mutane dubu 650 sun mutu a yakin Iran da Iraqi

Yayin da aka cika shekaru 40 da barkewar yaki tsakanin Iran da Iraqi, masana tarihi na ganin an tafka asarar rayukan mutane akalla dubu 650 kuma mafi yawansu Iraniyawa ne. 

Iraniyawa sun fi yawa cikin mamatan da aka samu a lokacin yakin tsakanin Iran da Iraqi a cewar masana tarihi
Iraniyawa sun fi yawa cikin mamatan da aka samu a lokacin yakin tsakanin Iran da Iraqi a cewar masana tarihi REUTERS / Yannis Behrakis
Talla

Jagoran addinin Iran Ayatollah Khomenei ya yi tsokaci kan yakin da kasashen biyu suka fafata tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1988, inda yake cewa idan kasa na da karfin kare kanta ta kowacce hanya, hakan zai sa abokan hamayyarta su sake tunani idan sun tashi takalar ta.

Khomenei wanda ya yi jawabi kai tsaye ya ce, yakin ya sa Iran ta kara karfin gaske fiye da yadda take a can baya.

Shugaban addinin ya soki kasashen yammacin duniya kan bai wa marigayi shugaba Saddam Hussein na Iraqi makamai , yayin da suka ki bai wa Iran agaji, al’amarin da a cewarsa ya nuna karara zaluncin kasashen yammacin.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai wani lokaci da Amurka ke shelan sabunta takunkumin karayar tattalin arziki kan Iran duk da cewa sauran manyan kasashen duniya sun yi fatali da barazanar.

A cikin shekara guda, sau biyu Amurka da Iran ke kusan bai wa hammata iska gadan-gadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.