Isa ga babban shafi
Amurka-China

Ba za mu jure sukar da Amurka ke mana kan coronavirus ba - China

China ta caccaki Amurka a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda take cewa ba za ta iya jurewa yadda take sukar ta kan annobar korona ba, saboda haka ta ci tuwon karshe.

Zauren kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.
Zauren kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Jakadan China a kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya Zhang Jun, ya ce Amurka ta haifar da matsaloli ga duniya, wajen batawa kasar suna da kuma yada labaran da babu gaskiya a ciki.

Zhang Yun yace Amurka ta samu mutane kusan miliyan 7 da suka harbu da cutar korona, yayin da mutane sama da 200 suka mutu, duk da cigaban fasahar da kasar ke tinkaho da shi a duniya, sakamakon gazawar da shugabannin siyasa suka yi wajen daukar mataki.

Yayin mayar da martani, Jakadiyar Amurka a Majalisar, Kelly Craft ta bayyana bacin ranta da irin kalaman da taji a taron da shugaban Nijar Mahamadou Issofou ya jagoranta, inda take cewa abin kunya ne irin kalaman dake fitowa daga Jakadun.

Craft ta bayyana bacin ranta da yadda taron kwamitin sulhun ya koma batun siyasa maimakon mayar da hankali kan matsalolin dake gabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.