Isa ga babban shafi
China

China ta je debo buraguzai a duniyar wata

Kumbon China ya isa duniyar wata da zummar debo samfurin buraguzan watan a karon farko cikin shekaru 40 kamar yadda Hukumar Sararin Samaniyar kasar ta bayyana.

Kumbon China na  Chang'e-5 da ya halarci duniyar wata domin debo buraguzai.
Kumbon China na Chang'e-5 da ya halarci duniyar wata domin debo buraguzai. Reuters
Talla

Kasar China ta zuba biliyoyin kudi cikin shirinta na sararin samaniya da sojojinta ke jagoranta, inda take burin samun fegi a duniyar wata nan da shekarar 2022 kafin daga bisani ta fara tura mutanenta can duniyar watan.

Burin China na halartar duniyar watan a wannan karo, shi ne kankaro wani bangare na tsaunukan da ke cikin watan domin taimaka wa masana kimiyarta zurfafa bincikensu game da usulin wata da kuma yanayinsa.

A wannan Talatar ne kumbon Chinan da aka yi wa lakabi da Chang-e 5 ya dira a kusa da duniyar watan kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar na Xinhua ya rawaito daga Hukumar Sararin Samaniyar kasar.

Muddin wannan balagoro na China ya samu nasara, kasar za ta kasance ta uku a duniya da ta bantaro samfurin wata bayan Amurka da Tsohuwar Tarayyar Soviet da suka samu makamanciyar wannan nasara a tsakankanin 1960 da 1970.

Kumbon na China ya isa duniyar watan ne bayan shafe tsawon sa’o’i 112 yana sharara gudu a sararin samaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.