Coronavirus na cigaba da gasawa Amurka, Brazil da India aya a hannu
Sabbin alkaluman da hukumomin lafiya suka fitar a yau asabar, sun nuna cewa yawan mutanen da annobar Covid-19 ta halaka a yanzu ya haura miliyan 1 da dubu 595, yayinda kuma adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura miliyan 71 da dubu 41.
Wallafawa ranar:
Sai dai akalla mutane miliyan 44 da dubu 731 sun warke.
Sabbin alkaluman sun ce a jiya Juma’a kadai, karin mutane dubu 702 da 77 aka gano sun kamu da cutar a fadin duniya, yayin da kuma annobar ta kalume rayukan wasu dubu 12 da 326.
Har yanzu Amurka ke kan gaba a tsakanin kasashen da annobar ta fi yiwa ta’adi bayan rasa akalla mutane dubu 295 da 539, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 180 da 437, yayinda kuma a India cutar da kashe mutane dubu 142 da 628.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu