Isa ga babban shafi
Trump-Amurka

Trump na shan caccaka kan yafiyar da ya yiwa karin masu laifi

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin afuwa ga aminansa da suka hada da mahaifin sirikinsa Jared Kushner da wasu mutane biyu da aka same su da hannu dumu-dumu a katsalandar din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Shirin afuwar na Donald Trump kari kan jerin mutane 26 da tun a baya ya yiwa afuwa kan batun yayinda ake sa ran nan gaba shugaban ya yi wa kansa da kansa afuwa da iyalansa da lauyansa Rudy Guiliani domin kare su daga fuskantar tuhuma.

Baya ga mahaifin sirikin na Trump Charles Kushner, sauran wadanda suka ci gajiyar shirin afiuwar na Donald Trump har da manajan kamfen dinsa Paul Manafort da dadadden mai bashi shawara Roger Stone.

Ko a talatar da ta gabata sai da Trump ya yi afuwa ga wasu mutane 15 ciki har da wani dan majalisar kasar da kuma jami’an tsaron kasar da ake tuhuma da kisan fararen hula 14 cikin shekarar 2007 a Baghdad.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan ya mika mulki ga Joe Biden da ya lashe zaben watan Nuwamba, yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan matakin afuwar na Trump.

Wasu dai na ganin matakin afuwar na Trump wani yunkuri ne na goge dukkannin hujjojin da ake dasu kan zargin kutsen da Rasha ta yi a zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.