Isa ga babban shafi
Iran-Iraqi

Ana zanga-zangar kisan da Amurka ta yi wa kwamandan Iran

Dubban al’ummar Iraqi da ke alhinin mutuwar kwamandan sojin Iran Qasem Soleimani na gudanar da zanga-zanga a yau Lahadi bayan cika shekara guda cur da kisan da Amurka ta yi masa a birnin Bagadaza.

Qasem Soleimani
Qasem Soleimani AFP Photos/Khamenei.IR via Handout
Talla

Akasarin masu zanga-zangar da suka yi dafifi a dandalin Tahrir sanye da bakaken tufafi, sun yi ta rera wake-wake, suna furta kalmar “ Ramuwar gayya”, yayin da suka caccaki Firaministan Iraqi, Mustafa al-Kadhemi, inda suka bayyana shi a matsayin matsoraci kuma wakilin Amurkawa.

A kwanakin nan aka gudanar da makamancin wannan bore a Iran da Syria da Lebanon da Yemen da wasu sassa domin tunawa da kisan da Amurka ta yi wa Soleimni ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuki a farkon shekarar bara, lamarin da ya kusan haddasa yaki tsakanin Washington da Tehran.

An dai zafafa wannan zanga-zangar ce a kasashen yankin gabas ta tsakiya a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan shugaba Donald Trump da ya bada umarnin kashe Soleimani ya sauka daga kujerar mulkin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.