Isa ga babban shafi
Covid-19

Sabuwar cutar Korona ta shiga kasashe 50 - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da cewa ya zuwa yanzu sabuwar nau’in cutar Coronavirus da ta bayyana a kasar Britaniya, ta shiga kasashen duniya 50, yayin da sabuwar nau’in cutar da aka samu a Africa ta kudu ta shiga kasashen duniya 20.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black / World Health Organization / AFP
Talla

Hukumar Lafiya ta duniyar ta kuma sanar da cewa akwai sabuwar nau'in wannan cuta ta corona, ‘yar Japan,  mai hatsarin gaske, wadda ta ke ci gaba da bincike sosai akan ta.

Hukumar na cewa binciken da ake gudanarwa na nuna cewa, sabuwar nau'in cutar ba ta haifar da tsananin rashin lafiya, amman kuma akwai ta da saurin yaduwa, alamarin da ke tada hankulan jami'an lafiya.

Hukumar ta ce yaduwar cutar bai kai yadda ake fadi ba, ganin yadda kasashen duniya ke gano mutanen da ke harbuwa da cutar a nasu yankunan.

A cewar Hukumar Lafiya ta duniyar kasar Japan ta sanar da ita ranar 9 ga wannan wata da muke ciki cewa ta gano sabuwar nau'in cutar yayin gwajin wasu mutane 4 da aka yi da suka fito daga Brazil, kuma masana a Brazil din su yi na'am da cewa suma suna binciken nau'in cutar sosai.

Ranar Talata ne dai jamian lafiya daga kasashen duniya 1,750 suka hadu don kara yin bincike mai zurfi game da wannan nau'in cutukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.