Isa ga babban shafi

Kussan biyu bisa uku na al'ummar duniya na cikin barazanar sauyin yanayi - MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace bincikenta ya gano kusan kashi 2 bisa uku, na mutane fiye da miliyan 1 da ta tuntuba a fadin duniya, na fuskantar matsalolin da sauyin yanayi ya haddasa. Binciken dai shi ne irinsa mafi girma da majalisar dinkin duniyar ta taba yi kan batun na sauyin yanayi.

Yadda al'umma ke gurbata yanayi
Yadda al'umma ke gurbata yanayi © Rim youth climate movement
Talla

Masana daga hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP da kuma taimakon wasu daga Jami’ar Oxford ne suka gudanar da wannan bincike, inda suka karbi ra’ayoyin mutane miliyan 1 da dubu 200 a kasashe 50 da suka kunshi sama da rabin yawan al’ummar duniya.

Wasu daga cikin kasashen kuwa sun hada da Amurka da Brazil da Rasha da Afrika ta Kudu da Faransa da kuma Jamus.

Binciken ya gano cewar kusan kashi biyu bisa uku na yawan mutanen sun bukaci daukar matakan gaggawa don kawo karshen barazanar da muhallin dan adam ke fuskanta daga jerin matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa, da suka hada da ambaliyar ruwa, guguwa, da kuma dumamar da wasu sassan duniya ke cigaba da yi.

Rahoton majalisar dinkin duniyar ya kuma ce kusan kashi 75 na adadin mutanen da ta tuntuba dake zaune a tsibbirai sun bada tabbacin cewar suna fuskantar barazanar rasa yankunansu sakamakon tunbatsar da tekuna ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.