Isa ga babban shafi
Myanmar

Kasashen Duniya sun yi tir da juyin mulkin Soji a Myanmar

Amurka ta jagoranci Gwamnatocin sassan duniya, wajen yin kira da a maido da gwamnatin dimokaradiyya a Myanmar, bayan da sojojin kasar suka kifar da ita a wani juyin mulki, suka kuma kama jagorarta, Aung San Suu Kyi.

Shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
Shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi. KHINE HTOO MRATT / AFP
Talla

A wata sanarwa, Kakakin fadar White House, Jen Psaki ta ce Amurka za ta sa kafar wando daya da wadanda suka yi wannan juyin mulki idan ba su jingine matakin na su ba, tana mai cewa Amurka ba za ta lamunci duk wani yunkurin jirkita sakamakon zaben watan Nuwamba wanda ya ba jam’iyyar Aun San Suu Kyi gagarumin rinjaye ba.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, wanda ya caccaki matakin sojin, ya ce ya zame musu wajibi su girmama tsarin dimokaradiyya, su kuma saki dukkanin jagororin fararen hula da suka kame.

China, wacce a kullum ta ke adawa da Majalisar Dinkin Duniya a kan Myanmar ta kira ta yi ga dukkanin bangarorin da su zauna a teburin shawara.

Majalisar Dinkin Duniya ta bakin sakatarenta, Antonio Guterres ta yi tir da matakin juyin mulkin da ma na garkame jagorar yankin.

Haka ma Tarayyar Turai, Japan da Australia dukkaninsu sun yi tir da yunkurin Sojin.

Ita ko Rasha, cewa ta yi, tana sa ido a al’amuran da ke gudana, inda ta ce yin tsokaci zai kasance tamkar riga malam masallaci.

Gabanin juyin mulkin, sai da Amurka da sauran kasashen yammacin Turai, a wata sanarwa, suka bukaci sojojin kasar da su girmama dimokaradiyya, bayan bbarazanar soke tsarin mulki da sojin suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.