Isa ga babban shafi
ICC

ICC ta share fagen soma bincikar Isra'ila kan aikata laifukan yaki a Falasdinu

Kotun hukunci kan manyan laifuka ta duniya ICC ta share fagen soma bincikar zarge-zargen da ake yiwa Isra’ila na aikata alaifukan yaki a falasdinu, bayan da a ranar Juma’a ta yanke hukuncin cewar tana da hurumin sauraron kararrakin da aka gabatar mata kan zarge-zargen take hakkin dan adam a yankin na Falasdinawa.

Babbar mai gabatar karar kotun duniya ta ICC Fatou Bensouda
Babbar mai gabatar karar kotun duniya ta ICC Fatou Bensouda Bas Czerwinski/Pool file via AP, File
Talla

Tun a watan Disamba na shekarar 2019, babbar mai gabatar karar kotun ta ICC Fatou Bensouda ta gabatar da kudirin neman kaddamar da cikakken bincike kan Isra’ila dangane da yankunan Falasdinawan da ta mamaye, da suka hada da gabashin birnin Kudus, Yamma da kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Yayin martani kan hukuncin, Isra’ila ta bayyana kotun ta ICC a matsayin kungiyar siyasa, yayin da Falasdinawa suka jinjinawa kotun, ita kuwa Amurka damuwa ta bayyana kan abinda zai biyo bayan matakin na ICC dangane da rikicin na Isra’ila da Falasdinawa.

A watana Oktoban 2020, Israila ta amince da shirin gina sabbin gidajen Yahudawa sama da dubu 2 a Yamma da Kogin Jordan, kwanaki kalilan bayan kulla yarjejeniyar hulda da wasu kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.