Isa ga babban shafi
Coronavirus-Duniya

Alkaluman wadanda Coronavirus ta hallaka ya zarta dubu 500- EU

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce adadin mutanen da annoba corona ta kashe ya zarce dubu 500 yanzu haka, yayin da ake cigaba da samun galabar cutar a wasu kasashen da ta yi wa illa.

Wani asibitin kula da masu Coronavirus a Amurka.
Wani asibitin kula da masu Coronavirus a Amurka. REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

Alkaluman da EU ta gabatar ya nuna cewa adadin mutanen da cutar ta kashe sun kai dubu 501 da 531 daga cikin mutane miliyan 20 da dubu 548,666 da suka harbu da ita.

Rahotan halin da ake ciki a yankin ya kunshi na kasashen da cutar tafi yi wa illa irin su Italia, yayin da ake cigaba da samun galabar cutar a kasashe da dama.

Rahotan da aka tattara kan cutar tsakanin ranakun 3 ga wannan wata zuwa 9 ga wata ya nuna cewar akalla mutane 103,250 ke kamuwa da cutar kowacce rana, wanda ya nuna raguwar kashi 16 daga abinda aka gani a makon jiya, yayin da aka samu mutuwar mutane akalla 3,137 kowacce rana, wanda ya nuna raguwar kashi 7 akan na makon jiya.

Daga cikin kasashen da suka fi shan radadin cutar akwai Spain da Jamus da Faransa da Sweden da kuma Italia.

A wajen kasashen EU kuwa Birtaniya da ke kasa at 5 a duniya da tafi jin radadin cutar yanzu haka ta na dauke da mutane 113,850 da suka mutu daga cikin miliyan 3 da dubu 972,148 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.