Isa ga babban shafi
Turkiya-Iraqi

Turkiya ta yi watsi da kalaman Amurka kan yadda mutanenta suka mutu a Iraqi

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya yi watsi da matakin Amurka da ke bayyana cewar 'yan ta’addan kungiyar Kurdawa ne ke da alhakin kai harin da ya halaka Turkawan da aka yi garkuwa da su a arewacin Iraqi.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya. Presidential Press Office/Handout via REUTERS
Talla

Tun farko sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken yayin zantawarsa da   takwaran ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ne ke shaida batun tare da mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin kasar.

Sai dai Tuni gwamnatin Turkiyan ta yi watsi da kalaman na Amurka yayinda ta gayyaci jakadan don bata bahasi kan yadda Turkawan 13 suka rasa rayukansu.

Gwamnatin Turkiya dai ta zargi Amurka da goyawa 'yan ta’adad baya wadanda suka kashe mata mutane 13 da aka yi garkuwa da su.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya fusata matuka da yadda mutanen 13 suka rasa rayukansu, yanzu haka ya yi sammacin Jakadan kasar David Satterfield domin nuna bacin ran sa.

Har zuwa yanzu dai Shugaban na Turkiya bai taya sabon shugaban Amurka Joe Biden murnar nasarar lashe zabe ba, saboda tsamin alakar da ke tsakanin Ankara da Jam'iyyar Democrat wadda Erdogan ke kallo a matsayin jagora a yakin Libya da ya daidaita ba kadai kasar ba har da makwabtan da sauran kasashen Larabawa da na Afrika, yakin da kuma ya taba manufofin Erdogan da dama da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.