Isa ga babban shafi
Syria

Sojojin Rasha sun kashe mayakan IS da dama a Syria

Sojojin Rasha su halaka mayakan kungiyar IS akalla 21 a yankin hamadar kasar Syria dake lardin Dier Ezzor.

Jiragen yakin kasar Rasha a Syria
Jiragen yakin kasar Rasha a Syria Russian Ministry of Defence/Olga Balashova/Handout via Reuters
Talla

Cibiyar Syrian Observatory dake sa ‘ido kan yakin kasar, tace dakarun na Rasha sun halaka mayakan na IS ne bayan luguden wuta sama da 130 da jiragen yaki suka yi kan wasu yankunan kasar ta Syria, dake zama maboyar ragowar mayakan na IS.

A shekarar 2014, kungiyar IS ta mamaye yankuna masu yawan a kasashen Syria da Iraqi, wanda daga bisani, rundunaonin sojin hadin gwiwa sun samu nasarar tarwatsa kungiyar.

Sai dai wani rahoton majalisar dinkin duniya, a baya bayan nan ya ce har yanzu akwai ragowar myakan IS kimanin dubu 10 a wasu yankunan Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.