Isa ga babban shafi
Saudiya - Amurka

Saudiya ta yi watsi da rahoton Amurka kan kisan Kashoggi

Kasar Saudiya tayi watsi da rahoton Amurka da ya  bankado cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na da masaniya kan  kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekarar 2018.

An dai gano Muhammad Bin Salman cike da murmushi yana daukar hoto da mahalarta taron duk kuwa da dambarwar kisan Jamal Kashoggi da ake yi kansa.
An dai gano Muhammad Bin Salman cike da murmushi yana daukar hoto da mahalarta taron duk kuwa da dambarwar kisan Jamal Kashoggi da ake yi kansa. SAUDI-BINLADIN/FALL Bandar Algaloud/Courtesy of Saudi Royal Cour
Talla

Cikin sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyan ta fitar jiya Jumma’a tace, kwata-kwata ta ki amincewa da karyar da rahoton na Amurka ya kunsa, wanda tace, ba abin lamunta ba ne.

A cikin wani rahoto da sabuwar gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta fitar jiya jumma’arce dai hukumar leken asirin kasar ta tabbatar da Yarima Bil Salman a matsayin wanda ya bada umurnin kama ko kuma kashe   Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiya dake Istanbul, na kasar Turkiyya.

To sai dai, duk da wasu jirin matakai da Amurka ta dauka kan wannan batu ciki harda hanawa wasu ‘yan kasar Saudiyan Visar shiga kasar, kasashen biyu na kokarin kaucewa saba alakarsu.

Dama dai, masana da kungiyoyin kare hakkin bil’ada sun daura alhakin kisan dan jaridar kan Yarima Mohammed Bil Salma, sai dai gwamnatin Saudiya tasha musanta zargin.

"Abin takaici ne kwarai da gaske ganin wannan rahoto na CIA, mara tushe balle makama, duk cewa masarautar Saudiya ta fito karara ta yi tir da wannan danyen aiki, kuma shugabannin masarautar sun dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa irin wannan bala'in bai sake faruwa ba," ta bakin  ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Ana zargin cewa an yauradi Khashoggi, mai sukar Yarima Mohammed, ne zuwa karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a cikin watan Oktoba na shekarar 2018, inda rundunar Saudiyya ta kashe shi.

Rahoton na Amurka ya ce babu yadda za’ayi wannan aika-aikar ba tare da sa hannun Yarima Mohammed ba, idan aka yi la’akari da tasirin sa .

Bayan fitowar rahoton, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce Washington na bukatan dai-dai ta al’amura ne, amma ba neman "rusa" dangantakarta da Riyadh ba, wacce ta kasance babbar abokiyar kawancen su a Gabas ta Tsakiya.

Duk da fushin da ta yi game da rahoton, Saudiyyar ta kuma jaddada cewa tana da muradin kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ma'aikatar harkokin wajen ta ce, "Hadin gwiwar da ke tsakanin Saudiyya da Amurka, kawance ne mai dorewa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.