Korea ta Arewa ta cilla wani shu'umin makami cikin teku
Sojan kasar Korea ta Kudu sun sanar da cewa makwabciyarta Korea ta Arewa ta cilla wani shu'umin makami cikin teku da duku-duku yau Alhamis wanda karon farko kenan tana cilla irin wannan makami a karkashin Gwamnatin Amurka ta yanzu wato Shugaba Joe Biden.
Wallafawa ranar:
Da jimawa kasar Korea ta Arewa na da dadadden tahirin gwajin shu’uman makamai da take kerawa.
Babban Hafsan sojan Korea ta kudu ya fadi cikin wata sanarwa cewa lallai makwabciyar nata ta harba makamin wanda basu tanttance irinsa ba.
Shima Firaministan Japan Yoshihide Suga ya fadi cewa makamai biyu Korea ta Arewa ta harba a yau alhamis.
Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai ganin irin tsokana da Korea ta Arewa ke ci gaba da yi tareda harba irin wadanan makamai ba bisa ka’ida ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu