Isa ga babban shafi
Saudiya-Umara

Rigakafin Korona ya zama dole ga masu Umara cikin azumi

Hukumomin Saudiya sun bayyana cewa, mutanen da suka karbi allurar rigakafin Covid-19 ne kawai za ta bari su ziyarci kasar domin gudanar da ibadar Umara a  cikin watan Ramadana mai zuwa.

Annobar Covid-19 ta tilasta daukar matakin rage cinkoson jama'a a Masallacin Ka'aba
Annobar Covid-19 ta tilasta daukar matakin rage cinkoson jama'a a Masallacin Ka'aba - Saudi Ministry of Hajj and Umra/AFP
Talla

Sanarwar da Ma’aikatar Kula da Hajji da Umara ta Saudiya ta fitar ta ce, mutanen da za a ba su damar gudanar da Umarar sun hada da wanda aka tsikara masa allurar rigakafin sau biyu da wanda ya karbi rigakafin sau daya da akalla kwanaki 14 kafin shiga kasar da kuma  mutanen da suka warke daga annobar.

Saudiya ta ce dole masu ibadar Umara su yi allurar rigakafin Covid-19

 

Wadannan nau’ukan mutanen da suka cika sharudan da aka gindaya, za a ba su damar gudanar da salloli  a babban Masallacin Ka’abah da ke birnin Makka da kuma Masallacin  Manzan Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam ) da ke birnin Madina.

Sanarwar ta ce, wannan sabon tsarin zai fara aiki ne daga watan azumi na Ramadana, wanda zai kama nan da kasa da makwanni biyu.

Sai dai babu cikakken bayani game da tsawon lokacin da za a dauka ana amfani da wannan sabon sharadin.

Kazalika hukumomin kasar ba su yi bayani kan ko sabon tsarin zai shafi aikin hajjin bana ba da za a gudanar wani lokaci a cikin wannan shekara ta 2021.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da cutar Covid-19 ta kashe mutane dubu 6 da 700  bayan ta harbi kimanin dubu 393 a kasar mai yawan jama’a miliyan 34.

Sama da mutane miliyan 5 aka tsikara wa allurar rigakafin Covid-19 a Saudiya kawo yanzu.     

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.