Har yanzu ba a kusanci nasarar kawar da annobar Korona ba - WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadin cewa ko kusa hukumomin kasashe basu yi kusa da samun nasarar kawar da annobar korona daga doron ka saba, sakamakon saba sharudda ko dokokin da kasashen da dama ke yi da gangan ko kuma saboda gazawa.
Wallafawa ranar:
Yayin ganawa da manema labarai a jiya Litinin, shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana rudani, rashin fahimtar munin cutar Korona, da kuma gaggawa wajen yin watsi da matakai ko sharuddan samun kariya saboda ikirarin samun nasara, a matsayin wasu daga cikin kura-kuran da ake tafkawa wajen yaki da annobar ta Korona.
Gargadin hukumar WHO na zuwa ne bayan da alkaluman hukumomin lafiya suka nuna cewar an bar kasashe matalauta a baya wajen aiwatar da shirin yiwa jama’a alluran rigakan Korona, kuma mafi akasarin wadannin kasashe suna nahiyar Afrika.
Kididdigar baya bayan nan ta nuna cewar mutane miliyan 13 aka yiwa allurar rigakafin cutar Korona a nahiyar ta Afrika, wadda yawan al’ummarta ya kai akalla biliyan 1 da miliyan 300.
A ranar Litinin ne kuma shugabar hukumar kasuwanci ta duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta ce kasa da mutane 3 cikin adadin ‘yan Afrika 100 ne kawai suka karbi allurar rigakafin Korona, a yayin da fiye da mutane 40 cikin adadin Amurkawa 100 ke samun allurar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu