Iraqi: An sake kai harin bam kan kasuwa a birnin Bagadaza
Hukumomin tsaro da na lafiya a Iraqi, sun ce akalla mutane 4 sun mutu, yayin da wasu 17 suka jikkata a yankin Sadr dake birnin Bagadaza, bayan tarwatsewar bam din da aka nada a wata mota a ranar Alhamis.
Wallafawa ranar:
Yayin karin bayani kan harin, ‘yan sanda sun ce an ajiye motar da ta tarwatse ne a wata kasuwar saida kayayyakin da aka taba amfani da su dake yankin da mabiya mazhabar shi’a suka fi yawa.
Harin na yau Alhamis na zuwa ne a yayin da ake hamayya ta zafafa tsakanin jam’iyyun siyasar Iraqi, sakamakon shirin fafatawar da suke yi a zabuka dake shirin gudana.
Har yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai farmakin, wanda shi ne na biyu mafi muni da aka kai a birnin Bagadaza a cikin wannan shekara, bayan wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da ya halaka akalla mutane 32 a wata Kasuwa cikin watan Janairu, da kungiyar IS ta dauki alhakinsa.
Harin na watan Janairu dai shi ne mafi muni da aka gani a babban birnin kasar ta Iraqi cikin shekaru 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu