Isa ga babban shafi
Amurka-Harin bindiga

Dan bindiga ya kashe mutane a Amurka

'Yan sanda a birnin Indianapolis na Amurka sun tabbatar da mutuwar mutane takwas bayan wani dan bindiga ya bude wuta kan mai-uwa-da-wabi.

Nau'ukan harsashen da 'yan bindiga ke amfani da su wajen kashe jama'a
Nau'ukan harsashen da 'yan bindiga ke amfani da su wajen kashe jama'a SPENCER PLATT GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP/File
Talla

Mai magana da yawun 'yan sandan Genae Cook ta tabbatar da aukuwar lamarin a wani gini da ke kusa da tashar jiragen sama, yayin da ta ce dan bindigar ya kashe kansa bayan ya yi kunar bakin wake.

Jami’ar ta ce maharin wanda ke rike da katuwar bindiga mai sarrafa kanta, ya harbi mutane da dama kafin mutuwarsa.

Hare-haren 'yan bindiga dadi na yawaita a Amurka, domin ko a karshen watan jiya, sai dai mutane hudu suka rasa rayukansu da suka hada da karamin yaro sakamakon harin na bindiga a kudancin jihar California.

Kazalika a ranar 22 ga watan Maris, mutane 10 sun mutu a harin bindiga da aka kaddamar kan wani katafaren shago da ke jihar Colorado, harin da ke zuwa kasa da mako guda da wani mutun ya hallaka mutane takwas a jihar Georgia ta irin wannan salo.

Alkaluma sun nuna cewa, kusan mutane dubu 40 ke rasa rayukansu a Amurka a duk shekara sakamakon hare-haren 'yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.