Isa ga babban shafi
Iraqi - Ta'addanci

An soma tattaunawa tsakanin Saudiya da Iran a Iraki

An soma wata tattaunawar sirri tsakanin kasashen Iran da Saudiya a kasar Iraqi.Bayanai na nuni cewa kusan mako daya kenan da aka soma wannan tattaunawa tsakanin jami’an diflomasiyar kasashen biyu.

Yarima  Mohamed Ben Salman
Yarima Mohamed Ben Salman AFP - HO
Talla

Manyan jami’an diflomasiyar kasashen Saudiya da Iran da ba sa ga maciji a baya sun samu ganawa a cikin wannan watan na Afrilu a binin Bagdaza na kasar ta Iraki.

Labarin da wani jami’in gwamnatin kasar Iraki ya tabbatar,sai dai  jami’in bai bayar da karin haske dangane da yada ganawar ta gudana.

Ranar lahadi da ta gabata ne jaridar kasar Birtaniya Financial Times ta wallafa cewa an samu ganawa tsakanin wakilan kasashen biyu ranar lahadi,sai dai a hukumance hukumomin Ryad sun musanta wannan labara ta kafar gwamnati ,yayinda kasar Iran ta gum ba tareda bada karin haske ba.

Tattaunawa tsakanin wakilan kasashen Iran,Iraki da wasu kasashen Duniya
Tattaunawa tsakanin wakilan kasashen Iran,Iraki da wasu kasashen Duniya © via REUTERS - EU Delegation in Vienna

Wasu rahotanni na dada nuni cewa ranar 9 ga watan Afrilun nan an hango wasu manyan jami’an diflomasiya da suka hada da Khalid Ben Ali al Humaidan daga Saudiya da Ali Chamkhani daga Iran a filin tashi da saukar jiragen kasar Iraki.

A shekara ta 2016 ne kasashen biyu suka yanke huldar diflomasiya tareda zargin juna da hadasa tashi hankali a gabas ta tsakiya.

To sai dai tattaunawa tsakanin kasashen zai kasance  mai amfani ga al’umomin su. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.