Isa ga babban shafi
Kimiya

Crew Dragon ya isa saman jannati

Tauraron dan adam mai suna Crew Dragon Endeavour mallakin SpaceX, ya isa sararin samaniya dauke da ‘yan sama jannati 4 ciki har da Thomas Pasquet dan asalin kasar Faransa.

Kumbon Crew Dragon
Kumbon Crew Dragon - NASA/AFP
Talla

Shi dai wannan tauroron dan adam din ya yi nasarar isa inda aka tura shi dauke da ‘yan sama jannatin a ranar Asabar da ta gabata, abin da ke matsayin gagarumar nasara ga cibiyar ISS mai zaman kanta da wani attajirin kasar Amurka mai suna Elon Musk ya kirkira.

Wannan ne dai karo na uku da wannan cibiya mai suna SpaceX mai zaman kanta ke harba tauraron dan adam zuwa sama, kuma Bafaranshe dan sama jannati Thomas Pasquet, ya ce ba wani abin fargaba dangane da wannan tafiya.

Shi dai Pasquet, ya yi wannan tafiya ne tare da wasu mutane uku, da suka hada da Shane Kimbrough, da kuma Megan McArthur ‘yan kasar Amurka, sai kuma Akihiko Hoshide dan kasar Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.