Isa ga babban shafi
Amurka-Baki

Amurka za ta rika karbar baki dubu 62 maimakon dubu 15- Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya amince da bai wa baki akalla dubu 62 da 500 damar shiga cikin kasar sabanin dubu 15 da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya amince da shi a lokacin mulkin sa.

Shugaba Joe Biden ya ce manufar Amurka ita ce maraba da baki masu amfani.
Shugaba Joe Biden ya ce manufar Amurka ita ce maraba da baki masu amfani. MANDEL NGAN AFP
Talla

Matakin ya biyo bayan suka da matsin lamba daga bangarori da dama saboda yadda shugaban ya amince ya yi aiki da adadin da Trump ya amince da shi a baya.

Sanarwar da shugaban ya gabatar ta ce wannan mataki mai dimbin tarihi ya share adadin da tsohuwar gwamnatin kasar ta amince da shi na dubu 15 wanda ya sabawa manufofin Amurka a matsayin kasar da ke karbar baki.

A wancan lokaci, Donald Trump zaftare adadin da ya tarar a lokacin gwamnatin Barrack Obama a wani yunkuri na hana kwararowar baki cikin kasar duk da yadda matakin ya sabawa tanade-tanaden kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.