Isa ga babban shafi
Isra'ila-Zabe

Bangaren adawa zai kafa gwamnati a Isra'ila bayan gazawar Netanyahu

Jagoran adawar Isra’ila Yair Lapid ya samu damar kafa gwamnati a kasar bayan gazawar Firaminista Benjamin Netanyahu na kafa gwamnatin hadakar har zuwa karewar wa’adin da aka dibar masa na tsakaddaren talata.

Sabon Firaministan Isra'ila mai jiran gado Yaïr Lapid.
Sabon Firaministan Isra'ila mai jiran gado Yaïr Lapid. REUTERS - AMIR COHEN
Talla

Isra’ila wadda ta gudanar da zaben ‘yan Majalisu har sau 4 a shekaru 2 saboda rashin rinjayen da Netanyahu ke samu a majalisar, wanda ya tilasta masa hada kai da abokin adawar sa Beny Gantz, ko da ya ke sun gaza kafa gwamnati saboda sharuddan da Netanyahu ya gindaya.

Shugaba Reuven Rivlin wanda tun a baya ke jan hankalin Netanyahu wajen ganin ya samar da kakkarfar hadakar don ci gaba da jan ragamar kasar, ya ce yanzu Lapid ke da damar iya kafa gwamnatin.

Kafin shugaban kasar ta Isra’ila ya sanar da sunan Lipid a matsayin magajin Netanyahu, an dauki tsawon sa’o’I 24 bayan karewar wa’adin da aka dibarwa Netanyahu ana tattaunawa da bangarorin jam’iyyun da kuma ‘yan majalisun da ke zauren.

Jam’iyyar Lapid ta masu sassaucin ra’ayi ta jima ta na zargin Netanyahu ya tayar da zaune tsaye a kasar baya ga rarraba kan jama’a.

Sabon Firaministan na Isra’ila wanda tsohon ma’aikacin gidan talabijin ne tun ba yanzu b aya sha alwashin kawo karshen mulkin Benjamin Netanyahu saboda yadda y ace jama’ar kasar na wahaltuwa karkashin mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.