Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Kasashen Larabawa sun yi Allah-wadai da Isra'ila kan muzgunawa Falasdinawa

Kasashen Larabawa sun yi A-wadai da Isra’ila kan rikicin baya bayan da Falasdinawa a Masallacin Al-Aqsa da yayi sanadin jikkatar mutane fiye da 250 a birnin Kudus.

'Yan sandan Isra'ila tsaye kan wani matashi Bafalasdine da suka tsare bayan tashin rikicin baya bayan nan a Masallacin Kudus.
'Yan sandan Isra'ila tsaye kan wani matashi Bafalasdine da suka tsare bayan tashin rikicin baya bayan nan a Masallacin Kudus. AP - Maya Alleruzzo
Talla

Sai dai a gefe guda Fira Ministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu da yayi watsi da caccakar ya sha alwashin maido da doka da oda a birnin na Kudus.

An dai shafe tsawon karshen makon da yak are ana arrangama tsakanin Falasdinawa da ‘yan sandan Isra’ila, lamarin da ya janyo jikkatar daruruwan mutane a rikici nasaba da takkadamar da bangarorin biyu ke yi kan wani yankin Falasdinawa da ke kusa da masallacin Al – Aqsa wurin da gwamnatin Isra’ila ke shirin mamayewa don tsugunar da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna.

Rikicin da ya jikkata Falasdinawa sama da 250 da ‘yan sandan Isra’ila kusan 20 dai shi ne mafi muni da aka gani a Masallacin Kudus tun bayan na shekarar 2017.

Wasu Falasdinawa dauke da 'yan uwansu da suka jikkata yayin arrangama da 'yan sandan Isra'ila.
Wasu Falasdinawa dauke da 'yan uwansu da suka jikkata yayin arrangama da 'yan sandan Isra'ila. AP - Oded Balilty

Tuni dai kasashen duniya suka fara tsokaci kan sabon rikicin na birnin Kudus inda dukkanin kasashen Larabawa 4 da suka maida huldar Diflomasiyya da Isra’ila a baya bayan nan, wato Hadaddiyar daular Larabawa, Morocco, Sudan da kuma Baharain suka turr da yadda gwamnatin Isra’ilar ta yi amfani da karfi kan Falasdinawa, wadanda suka ce suna tare da su.

A Jordan kuwa dauruwan masu zanga-zanga ne suka fita a babban birnin kasar Amman, inda suke neman a rufe ofishin jakadancin Isra’ila.

A yau litinin ne kuma ake sa ran kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya zai yi zama kan rikicin Falasdinawa da Isra’ila a birnin na Kudus da Masallacin Al Aqsa, kamar yadda kasar Tunisi ta tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.