Farmakin Isra'ila a kan Gaza ya halaka mutane sama da 40
Hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankin Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 40 a yau Lahadi, wanda shine adadi mafi muni na wadanda suka mutu a rana guda a kai- ruwa -rana da aka shafe kusan mako guda ana yi, a yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da taro a kan rikicin da ke ci gaba da ta’azzara.
Wallafawa ranar:
Yakin wanda shine mafi muni tun bayan shekarar 2014, wanda ya tashi sakamakon rikicin da ya auku a birnin Kudus, ya haddasa musayar wuta daga bangarorin da ba sa ga- maciji da juna, inda yanzu wadanda suka mutu suka kai 181 a yankin Gaza tun daga ranar Litinin, yayin da 10 suka halaka a bangaren Yahudawa, kamar yadda hukumomi suka sanar.
A Gaza, tawagogin ma’aikatan aikin agaji su na aiki tukuru wajen ciro gawarwakin mutane a baraguzan gine –gine da suka ruguje, a yayin da dangi da abokai ke kuka cikin makoki.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana takaici da yadda lamarin ke shafar akasari fararen hula, da kuma yadda Isra’ila ke kai hare -hare ba kakkautawa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu