Kungiyar Hamas da Islamic Jihad sun amince da shirin tsagaita wuta da Isra'ila
Israila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma Islamic Jihad sun bayyana amincewa da shirin tsagaita wutar da zai fara aiki daga karfe 2 na dare agogon yankin domin kawo karshen yakin da aka kwashe kwanaki 11 ana gwabzawa.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da ofishin Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya gabatar ta ce majalisar tsaron Israila ta amince ba tare da hamayya ba shirin kasar Masar na tsagaita wutar ba tare da gindaya sharidodi ba.
Suma kungiyoyin Hamas da Islamic Jihad sun tabbatar da shirin zagaita wutar da zai fara aiki daga karfe 2 na daren yau agogon Gabas ta Tsakiya.
Zuwa yanzu dai Falasdinawa 332 suka rasa rayukansu galibinsu fararen hula ciki har da mata da kananan yara, a luguden makaman roka fiye da 100 da Sojin Isra'ila suka harbawa yankin Gaza cikin kwanaki 11 da aka yi ana rikicin.
Haka zalika mutane fiye da dubu 1 da 600 suka jikkata yayinda ake fuskantar karancin abinci da magunguna a bangare guda kuma iyalai fiye da dubu 10 suka rasa matsugunansu sakamakon rushe-rushen da hare-haren na Isra'ila ya yiwa yankin.
Matakin tsagaita wutar ya biyo bayan kiraye-kirayen kasashen Duniya don daukar matakin Diflomasiyya da nufin shawo kan rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu