Isa ga babban shafi
Gaza - Isra'ila

Kasashen duniya sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugabannin duniya da manyan jami’an diflomasiyya sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki yau Jumma’a tsakanin Isra’ila kungiyar Hamas wacce kasar Masar ta shiga tsakani, yayin da suka bukaci warware rikicin na Gabas ta Tsakiya ta hanyar lumana mai dorewa.

Falasdinawa yayin murna a dauke da tutocin Hamas a harabar Masallacin al-aksa 21 ga watan Mayun 2021
Falasdinawa yayin murna a dauke da tutocin Hamas a harabar Masallacin al-aksa 21 ga watan Mayun 2021 AHMAD GHARABLI AFP
Talla

Baya ga maraba da matakin, Kungiyar Tarayyar Turai ta cikin wata sanarwa da shugaban diflomasiyasar ta Josep Borrellwata ya fitar, ta dage kan cewa "samar da kasashe biyu" shi ne kawai mafita na din-din-din.

Yayin da Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya yi gargadin cewa muddun ba’a ci gaba da tattaunawar ba, to babu shakka za’a koma gidan jiya.

Tallafi kudi ga Falasdinawa

Ita kuwa China kira tayi ga kashen duniya da su bada tallafin kudi ga Falasdinawa, inda tayi alkawarin bada dala miliyan daya na tallafin gaggawa ga Falasdinu, sai kuma Karin miliyan daya ga asusun agaji na MDD ga Falasdinawa.

Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce tsagaita wutar na nuna "sahihiyar dama" ga zaman lafiya biyo bayan tarzomar kwanaki 11 da yayi sanadiyar rasa dimbin ruyuka.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Heiko Maas wanda ya ziyarci Isra'ila da Ramallah don tattaunawa, yace dama ta samu na waiwayar musabbabin lamarin da kuma neman hanyar warware rikicin Gabas ta Tsakiya."

Sauran kasashen da suka yi maraba da matakin tsagaita wutan, har da Biritaniya da  da Kuwait.

Hezbollah

Kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon, wacce ke da kusanci da kungiyar Hamas ta masu kishin Islama, ta ce tsagaita wutar ta nuna "nasara mai dinbin tarihi".

Paparoma ya bukaci addu'o'in zaman lafiya

Yayin da Paparoma Francis ya yaba da tsagaita wutar tare da neman ilahirin Mujami'un Katolika da su yi addu’ar zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.