Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Al'amura sun fara komawa daidai a Zirin Gaza bayan tsagaita wuta

Masu shagunan shayi sun bude, masunta sun koma teku,  haka zalika masu shagunan kayayyakin masarufin sun fara shirye-shiryen budewa a yau Asabar, a yayin da al’ummar yankin Zirin Gaza ke komawa harkokinsu na yau –da-kullum sannu a hankali, bayan mummunan rikicin da aka shafe kwanaki 11 ana yi tsakanin mayakan kungiyar Hamas da Isra’ila.

Wasu masunta Falasdinawa da suka fito kamun kifi a Asabar 22 ga Mayu, 2021 bayan tsagaita wuta.
Wasu masunta Falasdinawa da suka fito kamun kifi a Asabar 22 ga Mayu, 2021 bayan tsagaita wuta. Emmanuel DUNAND AFP
Talla

Kayayyakin agaji sun fara isa yankin, wanda ke hannun kungiyar Hamas, a daidai lokacin da hankula suka koma kan batun sake gina yankin da ya tagayyara, kwana guda bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yarjejeniyar da Masar ta bijiro da ita, ta kawo karshen luguden wuta da Isra’ila ke yi a yankin da ke kunshe da dimbim Falsdinawa, da kuma harin roka da Hamas ke kai wa cikin Isra’ila tun daga ranar 10 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.