Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya-Belarus

MDD ta goyi bayan bincike kan tilasta wa jirgin sama sauka a Belarus

Babban Sakataren Majalisar Dinki Duniya Antonio Guterress ya  bayyana goyon bayansa ga kiran da ake na kaddamar da bincike mai zaman kansa  bayan da Belarus ta tilasta wa wani jirgin saman fasinja sauka tun kafin ya kai  inda za shi don kawai tana so ta kama wani mai adawa da gwamnatin kasar.

Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. Angela Weiss AFP/Archivos
Talla

Guterres ya kuma bayyana damuwa dangane da yadda batun kare hakkin dan adam ke tabarbarewa a Belarus, tun bayan zaben watan Agustan shekarar da ta gabata.

Mai Magana da yawun Sakataren Stephane Dujjaric ya ce yana bukatar ganin an gudanar da bincike mai zaman kansa da zai gano gaskiyar abin da ya faru, yayin da ya bukaci bangarorin da ke rikicin da su bada hadin kai.

Kasashe da dama sun bayyana damuwar su kann matakin da gwamnatin Belarus ta dauka na tilastawa jirgin sauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.