Ministocin G7 na nazari kan sabon tsarin haraji
Ministocin Kudi na kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na taro a birnin Landan, inda ake sa ran za su tattauna kan harajin da ake dora wa manyan kamfanoni. Taron wanda shugabar Baitul Malin Birtaniya Rishi Sunak ke jagoranta, zai kasance irinsa na farko tun bayan barkewar annobar Covid-19.
Wallafawa ranar:
Amurka ce ta mika bukatar a bullo da wani shiri da zai saukaka wa kananan kamfanoni, inda ake sa ran ministocin za su fi mayar da hankali kan karancin harajin da ake samu daga manyan kamfanoni na duniya.
Tuni kasashen Burtaniya da Jamus da Faransa suka yi maraba da wannan tsarin, inda suka nuna bukatar samar da mafita ga kamfanoni irin su Amazon, wanda ke da karancin riba fiye da sauran kamfanonin fasaha.
Shugaba Joe Biden ya yi kira da a yi duba kan mafi karancin harajin da bai wuce kaso 15 cikin dari ba, inda shugaban ke cewa babu yadda za a yi a karbi kaso mafi kankanta na haraji daga manyan kamfanoni a wasu wuraren.
Amurka na son kawo karshen harajin ayyukan fasahar sadarwa da kasashen Burtaniya, Faransa da Italiya suka karba, wanda kuma take kallo a matsayin ba daidai ba ga manyan kamfanonin fasahar Amurka don ayyukan haraji da kamfanonin Turai ke amfani da shi.
Abin da ake gani shi ne batun haraji na fasahar sadarwa ya zama fitila a cikin alaƙar kasuwanci tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu