Isa ga babban shafi
Faransa-Google

Faransa ta ci Google tarar Euro miliyan 200

Hukumomin Faransa sun ci tarar babban kamfanin sadarwa na Google Euro miliyan 220 bayan sun zarge shi da watsa tallace-tallace a shafin intanet  domin fifita kansa tare da yi wa aboban gogayyarsa zagon-kasa.

Google ya mamaye kasuwannin intanet a sassan duniya
Google ya mamaye kasuwannin intanet a sassan duniya REUTERS - Clay Mclachlan
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin na Google ke  ci gaba da fuskantar matsin lamba a nahiyar Turai.

Tarar wani bangare ne na jituwar da aka cimma, bayan wasu kafafen yada labarai uku na Turai da suka hada da News Corp da Le Figaro da Groupe Rossel sun zargi Google a 2019 da wuce-gona-da-iri wajen yin  kane-kane a kasuwar intanet ta hanyar mamaye tallace-tallace.

Hukumar da ke sanya ido kan gogayyar kasuwanci a Faransa ta  ce Google na fifita tallace-tallacensa tare da yin amfani da wasu dabaru na janyo hankulan kwastamomi don latsa tallace-tallacen nasa.

Kafafen yada labarai da ke neman kafar sayar da gurbin talla a shafukansu na intanet ko kuma manhajojinsu na kan wayar salula, sun fahimci cewa, Google na yi musu zagon-kasa domin kuwa shi ma yana gogayya da su a shafin na intanet.

Daga cikin abubuwan da Google din ke yi har da kankance tallace-tallacen takwarorinsa tare da bai wa kwastamomi wahala wajen latsa tallace-tallancesu, amma kuwa ba ya yi kansa haka.

Hukumomin da ke sanya ido kan gogayyar kasuwanci a Faransa sun ce, Google na nuna wannan halayyar ne domin danne sauran masu fafatawa da shi a fagen kasuwancin intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.